in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci nahiyar Afrika ta karfafa shirye-shiryen yaki da lalacewar dazuka
2018-10-03 15:48:34 cri
MDD ta yi kira ga dukkanin gwamnatocin nahiyar Afrika, su karfafa shirye-shiryensu na yaki da lalacewar dazuka da muhalli.

Jami'ar hukumar raya muhalli ta MDD Elsie Attafuah ce ta yi kiran, inda ta bukaci gwamnatocin su yi amfani da hadaddun dabarun da za su amfanawa al'ummomi.

Yayin wani taron karawa juna sani na nahiyar Afrika na bana, wanda da aka yi kan magance lalacewar dazuka a Nairobin Kenya, Elsie Attafuah, ta ce akwai bukatar daukar dabarun da za su ingantawa al'ummomi samun moriya daga albarkatun kasa ta hanyar shirye-shirye masu dorewa na amfani da filaye da rage lalacewar dazuka.

Ta ce dole ne dabarun su zama masu samar da sauyi da za su dace da yarjejeniyar rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli da kuma shirin yaki da sauyin yanayi.

Ta kuma jadadda bukatar hada gwiwa tsakanin gwamnatoci da bangarori masu zaman kansu, domin kawar da abubuwan dake takaita dabarun da ake amfani da su na yaki da lalacewar dazuka. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China