in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An karkare muhawarar babban taron MDD
2018-10-02 15:49:51 cri
A jiya Litinin shugabar babban taron MDD karo na 73 Maria Fernanda Espinosa Garces, ta jagoranci kammala muhawarar babban taron MDD, inda ta ce taron ya kammala cikin nasara.

A jawabin rufe taron da ta gabatar a gaban shugabannin duniya, Espinosa ta ce, "kowane mutum daga cikinmu zai fadi gaskiya cewa an kammala muhawara a babban taron MDDr cikin nasara tare da samun kyakkyawar gamsuwa."

Da ma dai an tsammaci shafe mako guda don gudanar da tsare-tsare da shirya ajandar da aka sanya gaba ta MDDr nan da shekara mai zuwa, madam Espinosa ta takaita sakamakon da aka cimma na babban taron zuwa guda 7, na farko ta ce ya mayar da hankali kan batun dunkulewar duniya wajen yin aiki tare domin sauke nauyin ayyukan MDDr da kuma kula da muhimmancin dake tattare da aikin gamayyar kasa da kasa a matsayin sahihiyar hanyar da za'a yi amfani da ita wajen tunkarar matsalolin dake shafar bil adama.

Na biyu, ta yi tsokaci cewa MDD gida ne ga kowace kasa a duniya, a makon da ya gabata an samar da yanayi ga kowace kasa da nufin zurfafa mu'amalar kasa da kasa da kuma kyautata alakar siyasa da kuma al'amurran da suka shafi kungiyoyin shiyya shiyya."

Na uku, shugabar taron MDDr ta ce, wakilan mambobin kasashen duniya sun yi musayar bayanai da kwarewa game da batutuwan dake shafar dukkan bangarorin, kuma an gudanar da wasu kananan taruka sama da 400 a gefen babban taron MDDr. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China