in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi bukukuwan musayar al'adun Sin da Rwanda
2018-07-08 16:37:51 cri
A jiya Asabar aka kammala bukukuwan musayar al'adu da nufin karfafa hadin gwiwar raya al'adun gargajiya da kafafen yada labarai tsakanin kasashen Sin da Rwanda da kuma kara bunkasa kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu wanda ya gudana a birnin Kigali helkwatar kasar Rwanda.

Taron dandalin hadin gwiwar yada labarai na Sin da Rwanda wanda aka bude da yammacin ranar Alhamis, an shafe kwanaki uku ana gudanar da shi a Kigali karkashin kulawar ofishin majalisar yada labarai ta kasar Sin (SCIO).

Bayan kammala dandalin kafafen yada labarun, an gudanar da bikin nune-nunen hotunan kasar Rwanda da na kasar Sin, wanda aka gudanar a safiyar ranar Juma'a a jami'ar Rwanda. An yi baje kolin hotuna sama da 80 na yankuna masu kayatarwa, da al'adun gargajiya na Sin da Rwanda, da nasarorin da aka cimma karkashin hadin gwiwa Sin da Rwanda, da kuma dandalin hadin gwiwa na Sin da Afrika.

Ana fatar mahalarta taron daga kasashen biyu zasu kara fahimtar yadda dangantaka take kara kyautatuwa tsakanin Sin da Rwanda da dogon tarihin kasashen, kana da nazarin sabbin hanyoyin da zasu kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, inji Guo, mataimakin darektan ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin.

An kaddamar da bikin nuna fina-finan kasar Sin a ranar Asabar wanda shi ne ke tabbatar da nasarar kammala bukukuwan na tsawon kwanaki uku.

Nuna fina-finan zai taimakawa jama'ar kasar Rwanda masu sha'awar kallon wasan kwaikwayo wajen kara fahimtar al'adun Sinawa kana zai kara bunkasa cigaban kamfanonin shirya fina finai na Rwanda da kasashen Afrika, inji Mr.Guo.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China