Kalaman shugaban na zuwa ne, baya da jaridar Herald da ake wallafa a kasar ta buda wani rahoto a jiya cewa, shugaba Mnangagwa ya shaidawa manema labarai bayan ganawa da sabon jakadan Amurka dake kasar ta Zimbabwe Brian Nicholas ranar Laraba cewa, ya kamata sabon jakadan da ya kama aiki a watan Yulin wannan shekara ya fahimci abin da ke faruwa a kasar.
Jakada Nicholas ya ziyarci Mnangagwa ne 'yan kwanaki bayan shugaba Donald Trump na Amurka ya sake kakabawa kasar takunkumi. Ya kuma bukaci kotun kundin tsarin mulkin kasar Zimbabwen da nuna gaskiya yayin da take sauraron korafin sakamakon zaben da jagoran 'yan adawar kasar na jam'iyyar MDC Nelson Chamisa ya gabatar mata.
Chamisa dai yana kalubalantar nasarar kaso 50.8 cikin 100 da aka ce Mnangagwa ya samu a zaben shugaban kasar da ya gudana, yayin da shi kuma ya samu kaso 44.3 cikin 100 na kuru'un da aka kada.(Ibrahim)