in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoto: Ghana ta yi nasarar rage kaifin talauci
2018-09-10 13:32:00 cri
Wani sabon rahoto ya nuna cewa kasar Ghana ta samu gagarumin cigaba wajen rage tsananin talauci tsakanin shekarar 2013 zuwa shekarar bara.

Kasar ta yammacin Afrika mai arzikin cocoa, zinare da albarkatun mai, ta kasance daya daga cikin kasashe na farko da suka samu tagomashi wajen rage kaifin talauci gabanin cikar wa'adin da aka debawa shirin nan na cigaban muradun karni wato MDGs nan da shekarar 2015.

Binciken ya kasance a matsayin wani mizani da aka yi amfani dashi a kasar ta Ghana cikin shekaru 30 kuma an yi amfani dashi wajen bibiyar yanayin walwalar jama'ar kasar da kuma irin cigaban da aka samu ta fuskar zamantakewa da tsare tsaren tattalin arzikin kasar.

Kwararrun masana sun yi tsokaci cewa duk da kasancewar an samu raguwar alkaluman girman talauci a kasar, amma akwai wagegen gibi wanda ke cigaba da karuwa na rashin daidaito a tsakanin jama'a.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China