Daga cikin wannan adadi, za a yi amfani da dala miliyan 48 da bankin duniya zai bayar wajen raya ayyukan inganta rayuwar jama'a, wadanda suka hada da samar da magewayi a gidajen jama'a da ma'aikatu a babban birnin kasar da a kalla mutane miliyan 3.7 za su iya amfani da su.
Za kuma a yi amfani da dala miliyan 45 da bankin raya Afirka(AfDB) zai bayar wajen gudanar da aikin tsaftar muhalli a yankunan karkara daga shekarar 2017 zuwa 2019, ciki har da gina wuraren bahaya 20,000 a gidajen iyalai a al'ummomi 500 a yankuna shida na kasar.
Hukumar lafiya ta duniya(WHO) da asusun tallafawa kananan yara na MDD(Unicef) da shirin nan na sanya ido(JMP) sun sanya kasar ta Ghana a matsayin kasa ta 7 da ba ta da magewayi mai kyau a duniya, inda kimanin kaso 14 cikin 100 na 'yan kasar ne kadai ke iya amfani da magewayi .(Ibrahim)