Ministan ya ce mahukuntan kasar sun dauki wannan mataki ne, sakamakon yanayi na zaman dar dar da ake fuskanta a yankunan kasar dake da rinjayen masu magana da Turancin Ingilishi, wadanda ke fafutukar kafa kasar Ambazonia. Tuni dai masu dauke da makamai na wadannan yankuna, suka sha alwashin gurgunta nasarar babban zaben kasar.
Mr. Nji ya kara da cewa, an dakatar da safarar kayayyaki, da mutane a daukacin yankunan ta kasa, da layin dogo, da kuma sama, tun daga karfe 6 na yammacin ranar Asabar din nan 6 ga watan Oktoba, ya zuwa 6 na yammacin ranar Lahadi 7 ga wata. Kaza lika an haramta duk wani taro na jama'a, sai dai fa idan a runfunan zabe ne, inda ake kada kuri'u.
Sama da 'yan kasar miliyan shida da dubu dari biyar ne, ake sa ran za su kada kuri'u a zaben shugaban kasar na gobe, kamar dai yadda hukumar zaben kasar ta tabbatar. (Saminu Hassan)