in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sanya dokar hana fita a yankunan Kamaru da ake magana da turancin Ingilishi masu fama da tashin hankali
2018-09-30 15:47:15 cri
Mahukunta a yankunan kudu maso yammaci da arewa maso yammacin kasar Kamaru da ake magana da turancin Ingilishi sun ayyana dokar hana zirga-zirga ta sa'o'i 48 gabanin bikin ayyana samun 'yancin kan yankunan da dakaru masu dauke da makamai suka shirya.

Gwamnan yankin arewa maso yammacin kasar Adolph Lele Lafrique ya sanar da cewa, daga yau Lahadi 30 ga wata zuwa Litinin 1 ga watan Oktoban, shekarar 2018, an takaita zirga-zirgar jama'a daga wani bangare na yankin arewa maso yammcin kasar zuwa wani na tsawon sa'o'i 48. Sannan za a haramta tarukan jama'a da ma taruwar fiye da mutane hudu.

Lafrique wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce an haramtawa duk kan shagunan sayar da kayan makulashe da barasa da gidajen rawa da ba su da lasisi gudanar da harkokinsu. Haka kuma tashoshin mota za su ci gaba da kasancewa a rufe, a hannu guda kuma za a dakatar da zirga-zirgar Babura zuwa wani lokaci.

A garin Bue, babban birnin yankin kudu maso yammacin kasar ma, hukumomin yankin sun sanya irin wannan doka ta hana zirga-zirga daga yau Lahadi 30 ga watan Satumba zuwa ranar 1 ga watan Oktoba.

Jami'in yankin Bue, Wokam Paul ya bayyana cewa, a tsawon wannan lokaci, dukkan kasuwanci da na sayar da barasa za su kasance a rufe, sannan za a dakatar da harkokin shakatawa kamar na al'adu, jin dadin jama'a ko wasanni. Sannan an haramta duk wasu nau'in harkokin sufuri na gwamnati ko sassan masu zaman kansu, da ma rufe tashohin mota. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China