Ahmad ya shaidawa manema labarai bayan ganawarsa da shugaba Paul Biya na kasar Kamaru cewa, hukumar CAF ba ta taba tunanin dauke gasar daga kasar ta Kamaru ba. Tun farko hukumar CAF ta tsara gudanar da gasar ce a kasar Kamaru, amma a makon da ya gabata sai hukumar ta ce za ta duba yadda kasar ta shirya game da daukar bakuncin gasar bayan kammala zaben shugabancin kasar.
Koda ya ke Ahmad ya ce, shawarar daukar bakuncin gasar ko akasin haka ya dogara ne ga kasar ta Kamaru, domin sune za su fada mana cewa sun shirya ko mu kara musu lokaci yanzu ba su shirya ba, domin su ne za su shirya gasar ba hukumar CAF ba.
A baya dai hukumar CAF ta nuna damuwa game da aniyar kasar Kamaru ta shirya gasar, inda ya ba da misali da jinkirin da aka samu wajen gina filayen wasanni da yadda fadan 'yan tawaye masu dauke da makamai ke ci gaba da karuwa a yankunan kasar da ake magana da turancin Ingilshi. (Ibrahim Yaya)