Yossi ya ce, al'amarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar a wani waje da ake kira "Memiam" dake babban titin Mbalmayo-Zoetele.
"An kwashe mutanen 17 da suka samu raunuka zuwa wani asibiti dake gundumar Mbalmayo inda aka ba su kulawa karkashin likitoci da ma'aikatan jinyya. Sai dai babu wanda ya mutu daga cikinsu. Mutanen sun samu kananan raunuka ne," in ji Yossi.
Ya ce, hadarin ba zai haifar da cikas game da gudanar da gasar ba.
"Tawagar 'yan wasan daga kasashen Rwanda da Burkina Faso tuni sun riga sun bar asibitin kuma a halin yanzu gab da isa Yaounde. 'Yan kasar Ivorycoast sun yanke shawarar ci gaba da shiga gasar. Raguwar 'yan wasan za su ci gaba da yin gasar," in ji Yossi. (Ahmad Fagam)