Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da gwamnan yankin Littoral Ivaha Diboua Samuel Dieudonne ya fitar jiya Litinin.
Wasu ganau a yankin sun ce an tura adadi mai yawa na sojoji da 'yan sanda zuwa Otel din Sawa, bayan an ji karar harbin bindiga a Otel din da yammacin jiyan.
Wani bidiyo da wani ya dauka cikin sirri, ya nuna dakarun bataliyar kai daukin gaggawa suna kwashewa tare da raka fararen hula fita daga Otel din.
'Yan sanda sun yi gaggawar garzayawa wurin tare da rufe shi, sai dai daga baya, Gwamnan ya sanar da cewa an buga kararrawar ne bisa kuskure.
An shiga fargaba a Douala bayan aukuwar lamarin, sai dai Gwamnan ya ce tuni aka dauki matakan da suka dace. (Fa'iza Mustapha)