Za dai a shafe makonni biyu ne a na yakin neman zabe, kafin a kada kuri'a a zaben shugabancin kasar a ranar 7 ga watan Oktoban wannan shekara.
Shugaban kasar mai barin gado Paul Biya kana jagoran jam'iyyar CPDM mai mulkin kasa, yana neman sabon wa'adin mulkin na shekaru 7 da zai ba shi damar kara zama a kan mulkin da ya shafe shekaru 36 a halin yanzu.
Dan takarar babban jam'iyyar adawa ta SDP, Joshua Osih ya kaddamar da yakin neman zabensa ne a Mbanga dake yankin Littotal. Osih dai yana ikirarin kafa tsarin tarayya a kasar ta Kamaru, domin kawo karshen matsalar tsaro da jin dadin jama'a a tsirarun yankunan kasar masu magana da turancin Ingilishi.(Ibrahim)