in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi kira da a hau teburin sulhu don warware batun nukiliyar Iran
2018-08-11 15:59:34 cri
Kasar Sin ta yi kira ga bangarorin masu ruwa da tsaki, su warware batun Nukiliyar Iran ta hanyar hawa teburin sulhu da tuntubar juna bisa tabbatar da adalci da mutunta juna.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya ce kasar Sin ta yi kiran dangane da sanarwar da Amurka ta yi na sake kakabawa Iran takunkumai a ranar Litinin.

Ya ce kasar Sin ba ta goyon bayan kakaba takunkumi bisa radin kai da shiga hurumin wani.

Har ila yau, Lu Kang, ya ce kasar Sin ta dade tana gudanar da huldar kasuwanci da Iran a bayyane kuma bisa adalci, a fannonin tattalin arziki da cinikayya da makamashi da sauran wasu fannoni, wadanda ba su take kudure-kuduren kwamitin sulhu na MDD ko kudurinta na kiyaye dokokin kasa da kasa ba, haka zalika ba ta taba raina muradun sauran kasashe ba, yana mai cewa, ya kamata a kiyaye tare da mutunta irin wannan hulda. (Fa'iza Msuatpha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China