in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Indiya suna son yin hadin gwiwa da kasashen Afirka domin cimma moriya da kuma nasara tare
2018-07-24 19:27:54 cri
A yau Talata, a yayin wani taron manema labaru da aka saba shiryawa kowace rana, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mr. Geng Shuang ta bayyana cewa, kasashen Sin da Indiya suna son kara yin hadin gwiwa da kasashen Afirka, a fannoni daban daban domin cimma moriya da nasara tare.

An labarta cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da firaministan kasar Indiya Narendra Modi, sun kai ziyara kasar Rwanda ne a rana daya, inda bi da bi, kasashen Sin da Indiya suka kulla wasu yarjejeniyoyin hadin gwiwa da kasar Rwanda.

A lokacin da yake ba da tsokaci game da makoma da kuma dama tsakanin kasashen Sin da Indiya a fannin yin hadin gwiwa a Afirka, Mr. Geng Shuang ya ce, "a matsayin su na kasashe masu tasowa, kuma masu samun saurin bunkasuwar tattalin arziki mafi girma a duk duniya, kasashen Sin da Indiya, dukkansu suna da niyyar taimakawa kasashen Afirka, wajen hanzarta bunkasa masana'antu, ta yadda za su iya neman samun ci gaba da kansu. Sannan suna da niyyar kara yin hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannoni daban daban, domin kokarin cimma moriya da nasa tare. A wannan batu, kasashen Sin da Indiya abokai ne da suke da shiri kusan iri daya."

Mr. Geng Shuang ya kuma bayyana cewa, shugaba Xi Jinping da firaminista Narendra Modi, za su gana da juna a lokacin da ake yin taron kolin kungiyar BRICS a kasar Afirka ta kudu. Wannan ne karo na uku da suka gana da juna a cikin 'yan watannin da suka gabata kawai, hakan ya bayyana cewa, huldar dake tsakanin kasashen Sin da Indiya tana samun ci gaba kamar yadda ake fata. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China