in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afrika ta kudu ya yabawa hadin gwiwar BRICS
2018-08-23 10:45:26 cri
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana a jiya Laraba cewa, hadin gwiwar mambobin kasashen BRICS ya baiwa Afrika ta kudu wasu muhimman damammaki wajen fadada harkokin cinikayyarta, da janyo hankalin masu zuba jari da kuma bunkasa tattalin arziki da kayayyakin more rayuwarta.

Huldar cinikayyar dake tsakanin kasar Afrika ta kudu da BRICS ya karu daga dala biliyan 28 zuwa dala biliyan 35 a cikin shekaru goman da suka shude, shugaban kasar ne ya bayyana hakan a yayin da yake mayar da martani kan batun rashin tabbas da wasu ke nunawa game da hadin gwiwar Afrika ta kudu da BRICS.

Da yake amsa tambayoyi a majalisar dokokin kasar a karo na biyu tun bayan da ya sha rantsuwar kama aiki a watan Fabrairu, Ramaphosa ya ce, mambobin kasashen BRICS su ne kashi 15 bisa 100 na kasashen da Afrika ta kudu take fitar da kayayyakinta kuma su ne kashi 25 bisa 100 na kasashen da take shigo da kayayyaki zuwa kasarta.

"Sabanin yadda manyan kasashen da suka ci gaba a duniya suke kokarin kare matsayin moriyar kamfanoninsu na cikin gida da bunkasuwar kamfanonin nasu, kasashen BRICS suna yin kokarin fitar da wasu tsare tsare ne na fadada cinikayya a tsakanin mambobin kasashen na BRICS a fannin ciniki da zuba" inji Ramaphosa.

A cewar shugaba Ramaphosa, daya daga cikin irin wadannan tsare tsare su ne na baje kolin kasar Sin na kasa da kasa na Shanghai wanda za'a gudanar a watan Nuwambar shekarar 2018, inda kasar Afrika ta kudu za ta yi amfani da wannan damar wajen baje kolin hajojinta da take fitar dasu zuwa kasar Sin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China