in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bakaken fata 'yan kasar Afrika ta Kudu sun samu nasarar mallakar filaye da amfani da su
2018-08-21 10:45:13 cri
Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya ce 'yan kasar bakaken fata sun samu nasarar mallakar filaye da ma amfani da su.

A kokarin rage fargabar da ake yi game da kudurin gwamnatin na karbar filaye ba tare da biyan diyya ba, Shugaba Ramaphosa ya ce 'yan kasar manoma bakaken fata, sun samu damar noma, don tabbatar da wadatar abinci da samun abun yi.

Shugban na wannan jawabi ne a wajen wani taro da Kungiyar Manoman Afrika reshen Afrika ta kudu ta shirya a Kempton dake lardin Gauteng, wanda ya mayar da hankali kan tabbatar da bakaken fata suna shiga ana damawa da su cikin hada-hadar kasuwancin a bangaren aikin gona. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China