in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Daliban Afrika ta kudu 32 ne suka samu guraben karatu karkashin tallafin gwamnatin kasar Sin
2018-08-17 10:39:25 cri

Dalibai 32 na kasar Afrika ta Kudu ne za su zo kasar Sin nan bada jimawa ba, domin karatun digiri na farko da na 2 da digirin digir-gir a kwasa-kwasai 17, karkashin tallafin gwamnatin kasar Sin.

Yayin bikin bankwana da aka yi wa daliban jiya a Pretoria, Jakadan kasar Sin a Afrika ta Kudu, Lin Songtian, ya bukaci daliban su zama jakadun kwarai na kawancen kasar Sin da Afrika ta Kudu.

Ya ce a yanzu, Afrika ta Kudu na samun dimbin damarmaki ta fuskar sauyin fasalin tattalin arziki da zaman takewa, wanda ke bukatar kwararrun jami'ai. A don haka suke fatan da daliban sun kammala karatu, za su koma su bautawa kasa da al'ummarsu domin bada gudunmuwa ga ci gaban kasar.

Ya kara da cewa, musayar mutane ya zama wani jigo na huldar dake tsakanin kasashen biyu. Inda ya ce hadin gwiwarsu a fannonin da suka shafi ilimi da al'adu da kimiyya da fasaha da kiwon lafiya da tallafawa matasa da mata, na ci gaba da fadada da samun tagomashi, wanda kuma ke kara inganta fahimtar juna da kawance tsakanin al'ummomin kasashen biyu.

Isasiphinkosi Mdingi mai shekaru 24, da ta fito daga lardin Eastern Cape, ta shirya tahowa kasar Sin a ranar 2 ga watan Satumba domin samun digiri na 2 a fannin nazarin manufofin gwamnati wato Public Admin, a Beijing.

Ta kuma shaidawa Xinhua cewa, za ta yi amfani da wannan dama wajen tabbatar da karin adadin mata na taka muhimmiyar rawa ga ci gaban kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China