Yayin da Cyril Ramaphosa ya isa birnin New York don halartar taron zauren MDD karo na 73, fadar shugaban kasar Afrika ta Kudu ta ce ana sa ran shugaban zai jaddada cewa, sauya tsarin mallakar filaye da Gwamnatinsa ta mayar da hankali kai, na da nufin inganta zaman lafiya da tafiya tare dukkan al'umma da kuma sauya tsarin tattalin arzikin kasar.
Taron na bana zai zama karon farko da Cyril Ramaphosa zai halarta a matsayin shugaban kasa.
Za kuma a dama da shi cikin muhawarar da ake yi duk shekara, inda shugabannin kasashen duniya ke haduwa a hedkwatar MDD domin tattauna batutuwan da suka shafi duniya baki daya.
Tun da Cyril Ramaphosa ya kama aiki a watan Fabrerun bana, Gwamnatin Afrika ta Kudu ta fara gaggauta aiwatar da shirin na sauya tsarin mallakar filaye, wanda ya kunshi kwace filaye ba tare da biyan diyya ba, abun da ya haifar da damuwa a ciki da wajen kasar. (Fa'iza Mustapha)