in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar kwadagon Najeriya ta janye yajin aikin neman sabon albashi
2018-10-01 15:57:03 cri
Hadaddiyar kungiyar kwadago a Najeriya ta sanar a jiya Lahadi cewa ta janye yajin aikin gama-gari da ta kira domin yiwa gwamnatin kasar matsin lamba sakamakon gaza biyan ma'aikatan kasar sabon tsarin albashi.

A jiya Lahadi ne hadaddiyar kungiyar kwadagon ta ayyana janyewa daga yajin aikin a duk fadin kasar na neman a biya 'ya'yanta sabon tsarin albashi.

A cewar shugaban kungiyar kwadagon kasar, Ayuba Wabba, matakin janye yajin aikin ya fara ne nan take.

Kungiyar kwadagon ta tsunduma yajin aikin ne tun a ranar Alhamis din da ta gabata bayan da gwamnatin ta gaza biyan muradun 'yan kungiyar cikin wa'adin kwanaki 14 da kungiyar ta baiwa gwamnati.

Wabba ya ce, matakin da kungiyar ta dauka na janye yajin aikin zai baiwa gwamnati damar amincewa da kwamitoci uku domin tattaunawa da su da kuma cimma matsaya game da batun aiwatar da sabon tsarin albashin ma'aikatan kasar.

Shugabannin kwadagon Najeriyar suna neman gwamnatin tarayya da ta biya su sabon tsarin albashi daga Naira 18,000 mafi karanci, zuwa Naira 56,000 mafi karanci, bisa la'akari da yanayin tattalin arziki da karuwar farashin kayayyakin masarufi a kasar. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China