Leah Sharibu ita kadai ta rage a hannu kungiyar Boko Haram, kana ita ce kadai Kirista cikin dalibai 'yan mata 110 na Sakandaren 'yan mata ta gwamnati dake garin Dapchin jihar Yobe dake arewa maso gabashin kasar, da kungiyar ta sace.
Muhammadu Buhari, ya wallafa jiya a shafinsa na Twitter cewa, ya yi magana da Rebecca Sharibu, mahaifiyar Leah, kuma ya tabbatar mata cewa gwamnati za ta dawo mata da 'yarta lafiya.
Ya ce addu'o'in 'yan Nijeriya na tare da iyalan gidan Sharibu, da ma sauran iyalan wadanda har yanzu suke hannun kungiyar. Yana mai cewa za su yi dukkan abun da za su iya don ganin sun 'yantar da su.
Rahotanni na cewa, wani tsagi na kungiyar Boko Haram ya ba gwamnatin kasar wa'adi zuwa ranar 15 ga wannan watan, don ta biya bukatar da ya gabatar mata game da sakin Leah ko kuma su kashe ta. (Fa'iza Msutapha)