in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya Ta Cika Shekara 58 Da Samun 'Yanci
2018-10-01 19:52:22 cri
Daga farko dai, taya al'ummar Najeriya murnar cika shekaru 58 da samun 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka. Bisa labarin da aka bayar yau a shafin intanet na jaridar Leadership A Yau ta Najeriya, an ce, a yayin da al'ummar Najeriya ke murnar wannan rana, shugabanni da 'yan kasa sun taya daukacin al'umma murnar zagayowar wannan rana.

A sakonsa na taya murna, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi 'yan Nijeriya da su yi amfani da wannan rana wurin addu'o'i ga kasa domin a samu hadin kai da kaunar juna.

Shi ma a nasa sakon na taya murna, Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Bukola Saraki ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su kasance masu aikata ayyukan da za su ciyar da kasar gaba, da kuma kauracewa duk wasu ayyuka da za su iya kawo cikas ga zaman lafiya.

Manyan mutane da masu ruwa da tsaki sun fitar da sakonnin taya murna ga al'ummar Nijeriya kan wannan rana ta cika shekaru 58 da samun 'yancin kai. Daga cikin wadanda suka taya 'yan Nijeriya murna akwai Tsohon Shugaban Kasa, Shagari da Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ekweremadu da wasu gwamnonin jihohi. gabadayansu sun bukaci 'yan kasa da su tsaurara kan addu'ar zaman lafiya, da rokon Allah ya sa a gudanar da zaben shekarar 2019 cikin kwanciyar hankali da lumana. (Sulaima Bala Idris na jaridar Leadership a Yau)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China