Hukumar kiddidiga ta kasar Sin, ta ce kasar ce ke da mafi yawan adadin masu fita kasashen ketare domin yawon bude ido.
Idan aka kwanta da miliyan 5 na shekarar 1995, kiddidiga ta nuna cewa, adadin tafiye-tafiye da Sinawa suka yi zuwa wasu kasashe a shekarar 2016 ya kai miliyan 135.
Wannan ya nuna cewa ana samun karuwar kaso 17.6 a kowace shekara cikin shekaru 21 da suka gabata.
Hukumar ta ce a kowace shekara tun daga 2013, kasar Sin ce ke kan gaba a yawan masu zuwa kasashen ketare domin yawon bude ido. (Fa'iza Mustapha)