in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Me ya sa ake da kwarin gwiwar zuba jari a kasar Sin?
2018-08-14 17:16:34 cri

Kungiyar cinikayya ta Amurka dake kasar Sin ta ba da rahoto kan yanayin ciniki da Sin ke ciki na shekarar 2018, inda ta ce a cikin shekarar 2017, kaso 73 cikin dari na kamfanonin Amurka sun samu riba a kasar Sin, yayin da kaso 74 cikin dari suka yi shirin habaka zuba jari a Sin a shekarar 2018, kuma mambobin kungiyar har kaso 60 cikin dari na daukar kasar Sin, a matsayi daya daga cikin wasu wurare uku da aka fi son zuba jari, kuma a ganin kamfanoni kashi 46 cikin dari, Sin za ta ci gaba da bude kasuwa ga kasashen waje a cikin shekaru uku masu zuwa. Wannan rahoton bincike ya bayyana cewa, galibin kamfanoni masu jarin waje wadanda suke nan kasar Sin suna cike da imani ga kasuwar kasar Sin, kuma za su ci gaba da zuba jari a kasar Sin. Me ya sa suke ganin haka? Ga dalilai biyar:

Na farko: Sin na da damar samun bunkasuwar samar da kayayyaki da saye-saye baki daya.

Na biyu: Sin na da rinjaye a dukkanin sha'anoni, wanda zai baiwa kamfanonin ketare goyon baya.

Na uku: Karfin samar da kayayyaki na Sin zai yi daidai da karfin kirkire-kirkire na kasashe masu wadata.

Na hudu: Farfadowar tattalin arzikin duniya sannu a hankali, za ta taimakawa kasar Sin wajen jawo karin jarin waje.

Na biyar: Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, bisa matakai masu amfani.

Bisa wadannan dalilai biyar, kasuwani mai girma, sha'anonin taimako masu kyau da Sin take da su, za su ci gaba da jawo hankalin masu zuba jari na kasashen ketare. Idan Sin ta ci gaba da samun bunkasuwa mai dorewa nan gaba. Babu dalili da a yi shakkar karfin jawo jarin waje da kasar Sin take da shi sakamakon takadammar ciniki. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China