in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Alkaluman matsakaicin sauyin farashin kayayyaki da kamfanoni suke fitarwa ya karu da kaso 4 bisa dari a Agusta
2018-09-10 15:18:45 cri
Ya zuwa watan Agusta da ya gabata, alkaluman matsakaicin sauyin farashin kayayyaki da kamfanoni suke fitarwa a nan kasar Sin, ya karu da kaso 4.1 bisa dari cikin tsawon watanni 12.

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ce ta bayyana hakan, tana mai cewa hakan ya yi kasa da karuwar kaso 4.6 da aka samu ya zuwa watan Yulin wannan shekara.

Babban jami'in kididdiga na hukumar ta NBS Sheng Guoqing, ya ce raguwar da aka samu na da nasaba ne da wasu alkaluma na gibi da aka samu na kaso 3 bisa dari a cikin jimillar kaso 4.1 bisa dari cikin watanni 12. Yayin da kuma wasu sabbin dalilai suka haifar da karuwar farashin kaso 1.1 bisa dari. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China