in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Me ya jawo hankalin masu zuba jarin kasashen waje zuwa nan kasar Sin
2018-08-20 16:28:46 cri
Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta bada alkaluma cewa, Sin ta kafa sabbin kamfanoni masu jarin ketare 35239 a cikin watanni 7 da suka gabata, wanda ya karu da kashi 99.1 cikin dari kwatan-kwacin makamancin lokaci na bara, yawan jarin ketare da aka yi amfani da su ya kai RMB biliyan 49.671, wanda ya karu da kashi 2.3 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.

A hanlin yanzu dai, Sin na jawo hankalin jarin ketare sosai duk da irin takadammar ciniki da halin tattalin arziki duniya mai cike da sarkakiya, mene ne dalili? Akwai su uku:

Na farko: Sin ta kan yi kokarin kyautatawa da daga matsayin halin shigo da jari da kawar shingaye.

Na biyu: Sin ita kadai na da wani rinjaye ta fuskar jerin sana'o'i da karfin samar da kayayyaki da rinjayen da take da shi a fannin kasuwanni, matakin da ya goyi bayan kamfanoni masu jarin ketare.

Na uku: Sin na da niyyar ci gaba da matakin bude kofa ga kasashen waje.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China