Mike Pompeo yana sanar da haka ne yayin wani taron manema labarai a jiya, inda ya ce mataki ne da ya kamata Amurka ta dauka shekaru 39 da suka gabata, yana mai cewa kasarsa za ta ga tasirin janyewar.
Da farko a jiya Laraba, kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC dake da mazauni a Hague, ta yanke wani hukunci kan takunkuman da Amurka ke sanyawa bisa radin kanta, biyo bayan janyewa da kasar ta yi daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, tana mai cewa dawo da takunkumai kan Iran da shugaba Donald Trump ya yi, ya sabawa ka'idojin yarjejeniyar dake tsakanin kasashen biyu. (Fa'iza Mustapha)