Gwamnatin Falasdinu, ta ce Amurka ta dakatar da duk wani nau'i na tallafi ga fararen hularta.
Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce Amurka ta yanke tallafin dala miliyan 500 a bana, inda ta ce daga cikin tallafin, ana amfani da dala miliyan 235 wajen gudanar da ayyukan da suka shafi tattalin arziki da jin kai a yammacin Kogin Jordan da na asibitoci a birnin Kudus da hukumomin Falasdinu, yayin da ake amfani da ragowar wajen gudanar da ayyukan hukumar MDD mai tallafawa Falasdinawa 'yan gudun hijira.
Gwamnatin ta soki yunkurin na Amurka, tana mai bayyana shi a matsayin yaki irin na rashin imani da ta kaddamar kan al'ummar Falasdinu da muradinsu.
Sai dai, sanarwar ta ce dukkan matakan da Amurka da Isra'ila za su dauka, ba za su taba dakatar da Falasdinawa daga kafa 'yantacciyar kasa a kan iyakokin da aka shata a 1967 tare da mayar da gabashin birnin kudus matsayin babban birninsu ba. (Fa'iza Mustapa)