Ban da wannan kuma, shahararren kamfanin kera wayoyin salula na Amurka wato Apple ya aike da wasika zuwa ga ofishin wakilin Amurka kan harkokin cinikayya, inda ya ce, idan Amurka ta sanya karin kudin kwastan kan hajojin kasar Sin da darajarsu ta kai dala biliyan dari biyu, za'a kara kudin da kamfanin zai kashe wajen yin kere-kere, abun da zai yi illa ga kamfanin wajen shiga takara da sauran kamfanonin duniya.
Dalilin da ya sa kamfanonin biyu, wato Ford da Apple, ba su son komar da masana'antunsu gida Amurka shi ne, muddin suka kera kayayyakinsu a kasar Sin, za su iya kara kwarewarsu wajen yin kere-kere gami da rage yawan kudin da za su kashe wajen yin kere-kere, ta yadda za su samu karin moriya, tare kuma da kara samun bunkasuwa.(Murtala Zhang)