in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanar da rufe ofishin PLO dake Washington
2018-09-11 10:16:54 cri
Sashen harkokin cikin gidan Amurka, ya sanar da rufe ofishin kungiyar dake fafutukar 'yantar da Falasdinawa ta PLO dake birnin Washington, bisa zargin sa da kin yin wani yunkuri na neman sulhu da Isra'ila, tare da hada kai da mahukuntan Falasdinu, wajen kai karar gwamnatin Isra'ila gaban kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC.

Cikin wata sanarwa da sashen ya fitar a jiya Litinin, ya bayyana rashin gamsuwa da yadda ofishin kungiyar ta PLO ya gaza, wajen gudanar da ayyukan sa yadda ya kamata.

To sai dai kuma a nasu bangaren, jami'an ofishin na PLO, wadanda tuni aka sanar da su kudurin na gwamnatin shugaba Trump, sun yi watsi da zargin na Amurka, suna masu cewa matakin nuna karfin tuwo ne kawai, da kuma yanke hukunci ba tare da yin cikakken nazari ba. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China