Wadannan kungiyoyin 150 suna wakiltar masu kera kayayyaki, da manoma, da masu sayar da kayayyaki, da kamfanonin kimiyya da fasaha, da kamfanonin gas da na man fetur, da masu shigo da kayayyaki, da masu fitar da kayayyaki da kuma sauran bangarorin da abun ya shafa.
A cikin wasikar da suka rubutawa wakili Robert Lighthizer, sun yi gargadi cewa, kara karbar haraji daga gefe guda, ba zai haifar da shawarwari masu ma'ana, ko rangwame ba, sai dai kawai ya jawo matakan mayar da martani.
Baya ga haka, kungiyoyin sun jaddada cewa, wadanda ke biyan haraji kan kayayyakin cinikayyar Sin, su ne kamfanoni da jama'ar kasar Amurka, a maimakon kamfanonin kasar Sin. (Bilkisu)