Sanarwar da ma'aikatar ta fitar a jiya, ta ce Stephen Biegun zai gana da takwarorinsa tare da ci gaban hadin gwiwar diflomasiyya domin cimma nasarar kawar da makaman baki daya, kamar yadda Shugaba Kim ya amince da shi a Singapore.
Shugaba Kim ya shaidawa wakilin Koriya ta Kudu a ranar Laraba cewa, zai goyi baya tare da tabbatar da ganin an kawar da duk wani hadarin yaki daga zirin Koriya, tare da mayar da shi dandalin zaman lafiya da babu makamai ko barazanar nukiliya.
Da yake mayar da martani a jiya Alhamis, Shugaban Amurka Donald Trump, ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa, yana godiya ga shugaba Kim bisa furucin da ya yi, inda ya ce za su tabbatar da aikin kawar da makaman nukiliya daga zirin Koriya a tare. (Fa'iza Mustapha)