in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya taya al'ummar Sinawa murnar cika shekaru 69 da kafa Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin
2018-10-01 15:21:10 cri
A jiya ne mai magana da yawun shugaban Najeriya Femi Adesina ya wallafa wasikar taya murna da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fitar mai dauke da sa hannunsa yana taya al'ummar Sinawa murnar cika shekaru 69 da kafa Jamhuriyar jama'ar kasar Sin a shafinsa na sada zumunta.

A cikin wasikar, shugaba Buhari ya bayyana cewa, a madadin gwamnati da al'ummar Najeriya, yana taya daukacin Sinawa murnar wannan rana mai muhimmanci. Ya kuma yaba da irin nasarorin da kasar Sin ta cimma cikin wadannan shekaru da ma kyakkyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Buhari ya kuma yi amfani da wannan dama wajen taya kasar ta Sin murnar nasarorin da ta cimma a fannonin tattalin arziki da fasahohi na zamani, da yadda kasar Sin take raba irin nasarorin da ta samu da kasashen Afirka da dama da ma sauran sassan duniya, lamarin da ya taimaka gaya wajen inganta rayuwar miliyoyin jama'a

Ya ce, jamhuriyar jama'ar kasar Sin babban kawar Najeriya ce. Don haka wajibi ne, mu kara hada kai da ita a fannonin tattalin arziki, da tsaro da kayayyakin more rayuwar jama'a da horas da ma'aikata.

Shugaba Buhari ya ce, a shirye Najeriya take ta kara zurfafa alakar moriyar juna da kasar Sin. Daga karshe muna muku fatan alheri, yayin da kuke muranr cika shekaru 69 da kafuwa. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China