in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyya mai mulkin Najeriya ta sahhalewa shugaba Buhari takarar shugabancin kasar a 2019
2018-09-30 15:58:06 cri
Jam'iyarr APC mai mulki a Najeriya ta amincewa shugaban kasar mai ci Muhammadu Buhari a matsayin mutumin da zai tsayawa jam'iyyar takarar shugabancin kasar a zaben shugaban kasar a shekara mai zuwa.

Ko da yake dama dai shi ne dan takara daya tilo da ya tsayawa jam'iyyar ta APC takarar, magoya bayan jam'iyyar ne suka bukaci a gudanar da zaben fidda gwamni na tsarin kato-bayan-kato wanda ya gudana a ranar Juma'ar da ta gabata, inda aka gudanar da zaben a duk fadin jahohi 36 na kasar.

Wani mai sharhi kan al'amurran siyasa a kasar ya ce, wannan tsarin zaben fidda gwani na kato bayan kato zai baiwa dukkan 'ya'yan jam'iyyar damar zabar wanda suke son ya zama dan takarar shugaban kasar a zabe mai zuwa.

A wata sanarwar da aka fitar a daren ranar Asabar, kakakin shugaban kasar Garba Shehu ya ce, an samu fitowar miliyoyin magoya bayan jam'iyyar a duk fadin kasar inda suka kada kuri'unsu, ya ce hakan ya tabbatar da irin tasirin da shugaban kasar ke da shi a zukatan 'yan kasar wanda ya baiwa jama'a kwarin gwiwa na kada kuri'unsu.

Ya kara da cewa, "Abu ne mai matukar muhimmanci kasancewar shugaba Buhari ya samu gagarumar nasara a zaben, zaben fidda gwamnin wanda aka gudanar kai tsaye a duk fadin kasar bisa adalci. Shugaban kasar ya nuna a fili cewa bai mallake jam'iyyar a matsayin tasa ba, kuma an kaucewa fuskantar wahalhalu wajen sasanto a cikin gida don fidda wanda zai tsayawa jam'iyyar takara," in ji Garba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China