A wata zantawar da ta yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ANC ta ce, a bayyane take karara cewa dakaru masu rajin sauya shugabancin kasar ba su amince ko kuma girmama 'yancin kasar da al'ummar kasar ta Venezuela ba, da kuma gwamnatin da aka zaba ta hanyar demokaradiyya.
Shugaba Maduro ya tsallake rijiya da baya daga wani yunkurin harin da aka kai masa ta jirgin sama marar matuki a ranar Asabar. A kalla wasu ababen fashewa biyu ne aka gano sun fado a gaban shugaban kasar daga cikin jirgin, a daidai lokacin da Mista Maduro ke gabatar da jawabin cika shekaru 81 da kafuwar rundunar tsaron kasar.
Maduro ya dora alhakin harin kan wasu dake yakar gwamnatinsa a cikin kasar ta Venezuela da kuma wata makarkashiya daga gwamnatin Amurka.
ANC ta yi Allah wadai da kakkausar murya da harin, ta kara da cewa, wannan kazamin aiki abu ne da ba za'a taba amincewa da shi ba a tsarin demokuradiyya da kuma masu son zaman lafiyar duniya.
Jamiyyar ANC ta bukaci gwamnatin Venezuela da ta binciko masababbabin harin kana ta yi dukkan kokarinta wajen kama wadanda ke da hannu kan lamarin.(Ahmad Fagam)