Amira Elfadil wadda ta bayyana haka a jiya, lokacin da take karban sabon Jakadan kasar Sin a Tarayyar Liu Yuxi, ta ce hukumar kula da ayyukan AU za ta taka muhimmiyar rawa ta hanyar shiga a dama da ita a taron da zai gudana da farkon watan Satumba a nan birnin Beijing.
A cewarta, FOCAC ya zama taron da ke gudana tsakanin Sin da Afirka akai akai, kuma akwai wani gagarumin aiki da hadin gwiwar bangarorin biyu zai samar karkashin taron na FOCAC.
Shugaban hukumar AU, Moussa Faki Mahamat tare da wasu manayn jami'an tarayyar ne za su halarci taron na Beijing, inda ake sa ran rattaba hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna a bangarori mabambanta.
Da yake ganawa da Xinhua, Jakada Liu ya ce yayin taron, shugabannin Sin da Afrika za su tattauna kan bangarorin da za su hada gwiwa kansu a shekaru masu zuwa. (Fa'iza Mustapha)