Moussa Faki Mahamat, ya bayyana matukar takaicinsa, game da rasa rayukan da aka samu, sakamakon hargitsin da ya biyo bayan fidda sakamakon babban zaben Zimbabwe da ya gudana a ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata.
To sai dai kuma ya yi maraba da matakan da mahukuntan kasar ke dauka, na tabbatar da gudanar da bincike, game da tashin hankalin da ya auku da nufin hukunta masu hannu a cikinsa. (Saminu Hassan)