Bikin na yini 5 da zai gudana har zuwa ranar 3 ga watan Augusta, zai samu mahalarta daban-daban daga kasashe mambobin Tarayyar Afrika AU.
Mahalarta daga kasashen da suka hada da Rwanda da Burkina Faso da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Senegal ne za su gudanar da wasanni a garuruwa daban-daban na Rwanda kafin rufe bikin a lardin Nyanza dake kudancin kasar.
Nahiyar Afrika na da albarkar al'adun gargajiya daban-daban da za a iya amfani da su wajen karfafa dunkulewarta da samar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin kasashe mambobin AU, Angela Martins, wakiliyar tarayyar Afirka ta fadi haka ne a wajen bikin.
Tarayyar AU ce ta kirkiro da bikin na FESPAD a shekarar 1998, da nufin hada kan al'ummar nahiyar da kuma inganta dabi'ar zaman lafiya ta hanyar raye-rayen gargajiya na nahiyar. (Fa'iza Mustapha)