Kwamishiniyar AU mai kula da bangaren walwala, Amira Elfadil, tace Sin da kasashen Afrika sun jima suna cin moriyar dadadden hadin gwiwar dake tsakaninsu.
Jami'ar ta yi wannan tsokaci ne bayan da ta karbi takardar kama aikin sabon jakadan kasar Sin a kungiyar tarayyar Afrika AU, Liu Yuxi, a jiya Alhmamis a helkwatar AU dake Addis Ababa na kasar Habasha.
"Dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika ba sabuwar dangantaka ba ce, matsayin dangantakar dake tsakanin AU da gwamnatin kasar Sin mai matukar karfi." inji kwamishiniyar.
Ta bayyana cewa hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin biyu ya shafi dukkan muhimman fannoni, da suka hada da fannin siyasa, zaman lafiya da tsaro, tattalin arziki, zuba jari, makamashi, hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya da cigaba da kuma kafa cibiyar riga-kafin yaduwar cutuka ta Afrika wato (Africa CDC).