in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Ghana na tattauna shirye-shiryen binne Kofi Annan da iyalansa
2018-08-21 10:38:32 cri
Gwamnatin Ghana na tattaunawa da iyalan Marigayi tsohon Sakatare Janar na MDD Kofi Annan, game da shirye-shiryen binne dattijon.

Mataimakin Ministan yada labarai na kasar Kojo Oppong-Nkrumah ne ya bayyana haka jiya Litini, inda ya yi alkawarin gwamnatin za ta bada dukkan taimakon da ake bukata don ganin an binne shi yadda ya kamata.

Ya ce suna tattaunawa don samar da hanyoyin tabbatar da an binne marigayin kamar yadda ya dace, musammam la'akari da matsayinsa a idon duniya.

Shi ma Shugaban Kasar Nana Akufo Addo, ya gana da iyalan marigayin a jiya, inda har ya sanya hannu cikin littafin ta'aziyya da aka bude domin girmama shi.

Gwamnati ma za ta bude littafin ta'aziyya domin tunawa da Marigayin da ya taba samun lambar karramawa kan zaman lafiya ta MDD, wanda ya rasu a ranar Asabar da ta gabata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China