in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya taya taron shekara-shekara na majalisar ICFHG murna
2018-09-28 21:00:37 cri
Yau Juma'a a nan birnin Beijing, aka bude taron shekara-shekara karo na 35 na majalisar tsoffin shugabannin gwamnatoci wato ICFHG a takaice, inda shugaban kasar kasar Xi Jinping ya aike da sako taya murna ga taron.

Xi ya nuna cewa, majalisar ICFHG na taka muhimmiyar rawa wajen neman hanyoyin tinkarar kalubaloli daban daban da duniya ke fuskanta, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da kuma inganta samun ci gaba tare. Ya kuma bayyana cewa, taron da ke mai da muhimmanci kan batun tafiyar da harkokin duniya, yana da ma'ana sosai, kuma zai amfanawa bangarori daban daban wajen zurfafa ra'ayin bai daya, da inganta kyautata tsarin tafiyar da harkokin duniya. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China