in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya jadadda bukatar aiwatar da dabarun bunkasa yankunan karkara
2018-09-22 20:09:48 cri
Shugaban kasar Sin, kuma Sakatare Janar na kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping, ya jadadda muhimmancin dake tattare da dabarun inganta yankunan karkara, wajen daukaka aikin gona da ciyar da manoma da ma yankunan gaba ta kowace fuska.

Xi Jinping ya bayyana haka ne yayin da yake jagorantar wani zaman nazari na hukumar kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS da ya gudana jiya Juma'a dangane da batun.

Ya ce dabarar bunkasa yankunan karkara manufa ce da aka ba muhimmanci yayin taron Jam'iyyar karo na 19, kana aiki ne mai muhimmanci da ya shafi samar da kasa mai tsarin gurguzu na zamani. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China