in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi ya yi kira da a bunkasa sana'ar sarrafa kayayyakin aiki
2018-09-28 10:36:50 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce ya kamata sana'ar kera kayayyakin aiki ta bunkasa kanta, musamman a lokacin da kasar Sin ke kokarin samar da ingantacciyar ci gaba, yayin da ake tsaka da ginin hanyar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.

Xi Jinping ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara CRRC Qiqihar Rolling Stock, Kamfanin kera kwantainonin dakon kaya mallakar gwamnati dake Qiqihar, birni mafi girma na 2 a lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin.

A matsayinsa na muhimmiyar bangaren tattalin arziki, akwai bukatar sana'ar kera kayayyakin aiki ta ci gaba da kokarinta na kirkire-kirkire, ta yadda za ta ci gaba da jagoranta aikin.

Shugaban na kasar Sin ya kuma kai ziyara kamfanin China First Heavy Industries mallakar gwamnati dake yankin, wanda ke kera manyan kayayyakin makamashin nukiliya da wadanda ake amfani da su a tashoshin samar da sinadarai daga man fetur da sauransu.

Ya ce kasar Sin ba ta taba kusantar cikar muradun da take son cimmawa yayin bukukuwa 2 na cika shekaru 100 da kuma fuskantar kalubale da wahalhalu irin yanzu ba.

Ya kara da cewa, kariyar cinikayya da daukar ra'ayi na kashin kai na karuwa a duniya, abun da ke tilastawa kasar dogara da kanta da kuma bin tafarkin juriya, wanda ya ce ba abu ne mara kyau ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China