A jawabinsa, Lin Jing ya ce, a shekarar da muke ciki, an yi nasarar gudanar da taron kolin dandalin tattaunawar hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a birnin Beijing, inda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya halarci taron, har ma ya gana da shugaban kasar Sin Xi Jinping. Hadin-gwiwar dake tsakanin Sin da Najeriya ta kasance abun misali ga hadin-gwiwar Sin da sauran wasu kasashen Afirka.
Shi kuma a nasa bangaren, mataimakin babban sakataren ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, Lawan Gana wanda ya halarci liyafar, ya bayyana cewa, bana shekaru 47 ke nan da kulla dangantakar diflomasiya tsakanin Sin da Najeriya, Najeriya na maraba da kamfanonin kasar Sin su zuba jari a kasar, kana tana fatan karfafa hadin-gwiwa da gwamnatin kasar Sin a fannoni daban-daban.(Murtala Zhang)