in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana da FIFA sun tattauna game da barazanar haramta kwallon kafa a kasar
2018-08-17 11:12:56 cri
Wakilan Ghana da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, sun gana jiya a hedkwatar hukumar dake Zurich na Switzerland, domin warware batutuwan da suka shafi yanayin da wasan kwallon kafa ke ciki yanzu a Ghana.

Ministan matasa da wasanni na Ghana, Isaac Kwame Asiamah, shi ya jagoranci wakilan kasar wajen ganawar dake da nufin neman farfado da wasan kwallon kafa da aka dakatar tsawon watanni 2 a Ghana.

Bayan tattaunawar, bangarorin biyu sun amince cewa, bisa tuntubar gwamnatin Ghana da hukumar kwallon kafa ta Afrika CAF, FIFA za ta kafa kwamiti da zai maye gurbin kwamitin zartarwa na Kungiyar kwallon kafa ta Ghana tare da nada mutane masu nagarta da kwarewa a matsayin mambobi.

Sanarwar da aka fitar bayan taron ta ruwaito cewa, Shugabannin Ghana da FIFA, sun kuduri niyyar aiki tare don jagorantar sake fasalin tsarin kwallon kafa a Ghana da Afrika.

Bangarorin biyu sun amince su yi aiki kafada-da-kafada, wajen fatattakar cin hanci da sauran laifuka daga harkar gudanar da kwallon kafa a Ghana, tare da samar da kwamitin hadin gwiwa da zai samar da shugabanci na kwarai da gudanar da bincike tare da tabbatar da an hukunta mutanen da aka samu da laifi bisa tanadin dokokin kasar da na FIFA. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China