Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartaswa ta kasa a Abuja babban birnin kasar, ministan albarkatun ruwa na kasar Suleiman Adamu, ya ce alamu sun nuna cewa ibtila'in ambaliyar ruwan ya zo karshe wanda ya shafi a kalla jahohin kasar 10.
Adamu ya ce, ruwan da ya tumbatsa daga madatsar ruwa ta Lagdo daga jamhuriyar Kamaru wanda ke makwabtaka da Najeriyar ya fara komawa daidai tun a ranar Asabar din da ta gabata, kuma wannan wata alama ce dake nuna cewa ruwan dake ambaliyar ya fara janyewa.
Ya ce adadin ruwan a Lokoja, wanda daya ne daga cikin biranen da ambaliyar ta yi mummunar barna, ya ragu da kusa sentimita 6 kuma yana ci gaba da raguwa.
A bisa ga kididdigar da hukumar bada agajin gaggawa ta kasar (NEMA) ta fitar, kimanin mutane 441,251 ne ambaliyar ruwan ta shafa daga kananan hukumomi 50 dake sassan Najeriyar.
A wani rahoton da aka fitar game da halin da ake ciki a ranar Litinin, hukumar bada agajin gaggawa ta kasar ta ce mutane 108 ne suka mutu sanadiyyar ambaliyar ruwan kana wasu 192 kuma sun samu raunuka. (Ahmad Fagam)