in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabaab 5 a yankin kudancin kasar
2018-10-01 15:29:49 cri
Rahotanni daga kasar Somaliya na cewa, sojojin kasar sun yi nasarar kashe mayakan al-Shabaab 5 tare da jikkata wasu da dama, yayin wani bata kashi da mayakan a yankin kudancin kasar dake kahon Afirka.

Kwamandan rundunar sojojin dake yankin Yusuf Hussein Osman, ya sanar da cewa sojojin da kuma dakarun dake yankin Jubba sun yi nasarar 'yantar da yankuna da dama yayin samamen da suka kaddamar a yankunan kimanin kilomita nisan kilomita 70 daga Kismayo, babban birnin yankin Jubba.

Osman ya kuma shaidawa manema labarai cewa, sojojin na kara samun nasara a samamen da suke kaddamarwa a yankin, inda suka yi nasarar kashe mayakan al-Shabaab guda 5 tare da jikkata wasu da dama. Sai dai kuma wasu sojoji biyu sun jikkata.

Ya ce, mayakan na al-Shabaab sun nuna turjiya sosai ta hanyar jefa wa sojojin makaman roka, amma daga bisani sojojin sun fi karfinsu. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China