Justin Brady, wanda jami'i ne a ofishin kula da harkokin jin kai na MDD, ya yi gargadin cewa, duk da yanayin samun abinci ya ingantu a kasar, har yanzu akwai wasu mutane masu yawa dake fuskantar rashin abincin.
Sanarwar da jami'in ya fitar a jiya, ta ce bukatun agajin gaggawa da al'ummomi daban-daban ke fuskanta akai-akai, ya sa sun kasa farfadowa. Sannan samun kudin agajin jin kai da zai shafe shekaru da dama abu ne mai matukar wahala.
A cewar UN, duk da ana samun ruwa da ya zarce matsakaicin mataki a lokutan damuna 2 da ake da su, akwai mutane miliyan 4.6 ciki har da yara miliyan 2.5 dake bukatar agajin jin kai. (Fa'iza Mustapha)