in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Somaliya sun hallaka mayakan al-Shabab 10 a tsakiyar kasar
2018-07-05 09:41:00 cri

Rundunar sojin kasar Somaliya (SNA) ta sanar cewa, dakarunta sun yi nasarar kashe mayakan al-Shabab 10 kana sun jikkata wasu da dama a wani mummunan dauki ba dadi da suka yi a garin Haradhere dake yankin Mudug a tsakiyar Somaliya.

Mahad Hassan Mohamed, mataimakin ministan jahar Galmudug a kasar Somaliya, ya ce fadan ya barke ne bayan da 'yan tawayen suka yi yunkurin kwace kudade da sace yara da nufin shigar da su ayyukan ta'addanci, sai dai mutanen kauyuka sun ki amincewa da yunkurin nasu.

Wani mazaunin yankin, wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya ce, an kashe mazauna kauyensu 5 da mayakan al-Shabab 10 a lokacin da aka yi fafatawar.

Mayakan Al-Shabab sun bayyana cewa su ne ke da nasara a kazamin fadan da aka gwabza na baya bayan nan a yankin Mudug, inda suka yi ikirarin hallaka dakarun tsaro 15 a jihar Galmudug.

Sai dai ministan ya tabbatar da cewa, an gwabza yakin ne tsakanin mayakan al-Shabab da mazauna yankunan, ya ce a shirye suke su baiwa ja'amarsu kariya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China