in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Somaliya sun lalata cibiyoyin mayakan al-Shabab dake kudancin kasar
2018-07-23 12:35:40 cri

Kwamandan sojojin Somaliya Mohamed Mohamud Gutale, ya sanar da cewa, sojojinsu sun yi nasarar lalata cibiyoyin mayakan al-Shababa dake kusa da garin Qoryoley dake garin lower Shabelle na kudancin kasar.

Kwamandan wanda ya bayyana hakan ta gidan rediyon kasar, ya ce sojojin sun kuma yi nasarar damke wasu daga cikin mayakan yayin harin da suka kaddamar kan manyan tungayensu, baya ga naurorin da mayakan ke amfani da su wajen hada abubuwa fashewa da aka lalata. Sai dai kuma bai yi karin haske ba game da adadin mayakan da sojojin suka kama ko sojojin da suka jikkata, ko kuma akwai abokan hulda na kasa da kasa da suka taimaka musu wajen kai harin

Gutale ya ce, a watan Janairu ne mayakan na al-Shabab suka yi amfani da nakiya wajen lalata daya daga manyan gadoji biyu dake garin Qoryoley. Gadar dai tana da matukar muhimmanci ga harkokin zirga-zirgar jama'a da kayayyaki a yankin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China