in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun hadin gwiwa na AU da Somali sun hallaka mayakan al-Shabaab 35
2018-09-25 10:59:39 cri
Kimanin mayakan kungiyar al-Shabaab 35 aka hallaka da kuma jikkata wasu da dama bayan musayar wuta tsakaninsu da dakarun sojojin gwamnatin Somaliya wadanda ke samun taimakon dakarun tsaron kungiyar tarayyar Afrika AU a garin Qoryoley, a shiyyar Lower Shabelle, dake kudancin Somalia, in ji jami'in kasar Somaliya.

Guda daga cikin sojojin Somaliya ya rasa ransa kana wasu sojojin biyu kuma sun samu raunuka a lokacin da aka yi mummunar arangama da mayakan na al-Shabaab a cikin dare, mataimakin gwamnan lardin Qoryoley, Abdi Ahmed Ali ne ya bayyana hakan ga manema labarai. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China